Hausa translation of the meaning Page No 58

Quran in Hausa Language - Page no 58 58

Suratul Al-Imran from 62 to 70


62. Lalle ne wannan, haƙĩƙa, shi ne lãbãri tabbatacce, kuma bãbu wani abin bautawa fãce Allah, kuma lalle ne, Allah, haƙĩƙa,Shi ne Mabuwãyi Mai hikima.
63. To, idan sun jũya bãya, to, lalle Allah Masani ne ga maɓannata.
64. Ka ce: « Yã ku Mutãnen Littãfi! ( 1 ) Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa ( 2 ) a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah. » To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: « ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne. »
65. Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta?
66. Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba!
67. Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
68. Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a ( zamaninsa ) da wannan Annabi ( Muhammadu ) da waɗanda suka yi ĩmãni.Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai.
69. Wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi sun yi gũrin su ɓatar da ku, to, ba su ɓatar da kõwa ba fãce kansu, kuma bã su sansancewa!
70. Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuka kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa kũ, kuna shaida ( cẽwa sũ gaskiya ne ) ?
( 1 ) Mutãnen Littãfi sũ ne Yahũduda Nasãra kõ da yake an ƙãre magana ne a kan Ĩsã, dõmin kira zuwa ga addini mai aƙĩda sahĩhiya ya haɗa kõwanensu.
( 2 ) Kalma mai daidaitãwa ita ce kalmar shahãda dõmin tã tabbatar da cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah. Bauta ita ce bin wani ga hukunce- hukunce na wajabtãwa kõ haramtãwa kõ halattãwa ko sanya wasu sharuɗɗa waɗanda sharĩ'a ba ta zo da suba. Wannan ãyã ba ta tsaya ga Yahũdu da Nasãra waɗanɗa suka ɗauki Ahbãr da Ruhbãn da mãsu ƙirƙira wasu hukunce- hukunce ba. A'a tã kai har ga Musulmi mãsu raunin hankali da ĩmãni, waɗanda suke zaton waliyyai sunã iya cũtãrwa, kõ sunã iya amfãnin wani da zãtinsu, kuma sunã iya halattãwar abin da Allah Ya haramta, kuma sunã iya haramtãwar abinda Ya halatta, tãre da haka kuma sunã ƙãga bidiõ'ĩ mãsu girma waɗanda Allah bai saukar da wani dalĩli a kansu ba, sunã sanya waɗannan bidi'õ'ĩ zama ɗarĩƙu ga waɗannan waliyyan. Sunã riya cẽwa sũ ne mãsu cẽton mutum kõ da suke sunã sãɓã wa sharĩ'a, sunã zaton cẽwa sunã kan wani abu. To, sũ ne maƙaryata, Shaiɗan yã rinjãye su har ya mantar da su daga tuna Allah. Waɗannan sũ ne ƙungiyar Shaiɗan. ( Dubi Sãwi ) .