Hausa translation of the meaning Page No 600

Quran in Hausa Language - Page no 600 600

Suratul Al-'Adiyat from 10 to 8


10. Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
11. Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?
Sũratul ƙãri‘ah
Tana bayãnin Rãnar Ƙiyãma wajen hãlin fitar mutãne daga kaburbura da hãlãyen ƙasa da rabuwar mutãne bãyan hisãbi wasu zuwa Aljanna wasu zuwa wuta, a bãyan bũsar ƙaho ta biyu
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Mai ƙwanƙwasar ( zukata da tsõro ) !
2. Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
3. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
4. Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
5. Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
6. To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
7. To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
8. Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi ( bãbu nauyi ) .
9. To, uwarsa Hãwiya ce.
10. Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
11. Wata wuta ce mai zafi.
Sũratut Takãthur
Tana bayãnin hana alfahari, sabõda dũkiya ko dangi.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku ( dagaibada mai amfaninku ) .
2. Har kuka ziyarci kaburbura.
3. A'aha! ( Nan gaba ) zã ku sani.
4. Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
5. Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
6. Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
7. Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
8. Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar ( da aka yi muku ) .