Hausa translation of the meaning Page No 599

Quran in Hausa Language - Page no 599 599

Suratul Al-Bayyinah from 8 to 9


8. Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa.
Sũratuz Zalzalah
Tana karantar da yadda mõtsin Tãshin Ƙiyãma yake, da bai wa mutãne sakamakon ayyukansu.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3. Kuma mutum ya ce « Mẽ neya same ta? »
4. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5. cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6. A rãnar nan mutane za su fito dabam- dabam domin a nuna musu ayyukansu.
7. To, wanda ya aikata ( wani aiki ) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.
Sũratul ‘Ãdiyãt
Tana karantar da yadda ake yin hari da lõkacin da ake yaƙin kãfirai, dã dalilin da ya sa a yãƙe su.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
2. Mãsu ƙyasta wuta ( da kõfatansu a kan duwatsu ) ƙyastawa.
3. Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
4. Sai su motsar da ƙũra game da shi.
5. Sai su shiga, game da ita ( ƙũrar ) , a tsakãnin jama'ar maƙiya.
6. Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
7. Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
8. Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
9. Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.