Hausa translation of the meaning Page No 70

Quran in Hausa Language - Page no 70 70

Suratul Al-Imran from 154 to 157


154. Sa'an nan kuma ( Allah ) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: « Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin? » Ka ce, « Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne. » Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: « Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan. » Ka ce: « Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu; » kuma ( wannan abu yã auku ne ) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
155. Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri.
156. Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: « Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba. » ( Wannan kuwa ) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne.
157. Kuma lalle ne idan aka kashe, ku a cikin hanyar Allah, ko kuwa kuka mutu, haƙĩƙa, gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.