Hausa translation of the meaning Page No 71

Quran in Hausa Language - Page no 71 71

Suratul Al-Imran from 158 to 165


158. Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku.
159. Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara ( 1 ) da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.
160. Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.
161. Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu. ( 2 ) Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar Ƙiyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.
162. Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita!
163. Sũ, darajõji ( 3 ) ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa.
164. Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala ( 4 ) a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya.
165. Shin kuma a lõkacin ( 5 ) da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: « Daga ina wannan yake? » Ka ce: « Daga wurin rãyukanku ( 6 ) yake. » Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.
( 1 ) Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su.
( 2 ) Gulũlu shĩ ne satar wani abu daga ganimar yãƙi agabãnin raba ta a tsakãnin mayãka. Allah Yã ce, « Yin gulũlu haram ne a kan kõwane annabi ko da waɗanda ba a halatta wa cin ganima ba, balle ga wanda aka halatta wa.Kamar yadda gulũlu yake haram a kan annabãwa haka yake haram a kan mabiyansu. »
( 3 ) Mũminai mãsu darajõji ne a wurin Allah gwargwadon ĩmãninsu da taƙawarsu da kuma falalar da Allah Ya yi musu. Haka sũ kuma kãfirai sunã da magangara zuwa ƙasa gwargwadon mugun aikinsu.
( 4 ) Allah Yã nũna falalar da Ya bai wa Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da yake har yanã yi wa mũminai gõri da kyautar da Ya yi musu ta hanyar aiko musu shi.
( 5 ) Duk masĩfar da ta sãme ku, tõ, ku ne kuka jãwo wa kanku ita da wani laifi na sãɓã wa umurnin Allah. Kuma kãmin masĩfa guda ta sãme ku, to, alhẽri biyu sun sãme ku.
( 6 ) Kowace irin masĩfa ta sãmi mutum, to, shĩ ne ya yi sababinta a kansa. Kuma yã kamata ya yi bincike ya gãne sababin, a inda ya jãhilce shi. Kuma duk da haka kãmin masĩfa guda ta sãme shi, ya sãmi ni'ima biyu kõ fiye da haka.