Hausa translation of the meaning Page No 69

Quran in Hausa Language - Page no 69 69

Suratul Al-Imran from 149 to 153


149. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗa'aga waɗanda suka kãfirta zã su mayar da ku a kan dugãduganku, har ku jũya kunã mãsu hasãra.
150. Ã'a, Allah ne Majiɓincinku kuma ShĨ ne Mafi alhẽrin matai maka.
151. Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai!
152. Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa ( 1 ) , kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan ( Allah ) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai.
153. A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku. ( 2 ) Sa'an nan ( Allah ) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
( 1 ) A lõkacin da aka fãra YãƙinUhdu Musulmi suka fãra kõra sunã kisa sunã kãmu. Sai wasu maharba suka ce: « Kada a kãme ganĩma a bar mu, » Shugabansu Abdullahi bn Jubair ya ce musu, « Ku tuna da maganar Manzon Allah da ya ce kada mu bar wurinmu sai idan shi ne ya kirãye mu. » Sai suka ƙi saurãran maganarsa suka tafi kãmun ganima. Sai Allah Ya biyõ musu da Khãlid bn walĩd ta bãya, ya kashe Abdullahi da sauran waɗanda suka rage. Sa'an nan kuma sai yãƙĩn Musulmi ya karye, suka gudu suka hau dũtse, sai mutum gõma sha ɗaya ko shã biyu kawai aka bari tãre da Annabi, yana kiran su sunã gudu.
( 2 ) Bãyan da hankalinsu ya kõma gare su sai suka ga sakamakon sãɓã wa umurnin Allah, ya zama karyẽwar yãƙi da rashin ganĩma.