Hausa translation of the meaning Page No 72

Quran in Hausa Language - Page no 72 72

Suratul Al-Imran from 166 to 173


166. Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin ( Allah ) Ya san mũminai ( na gaskiya ) .
167. Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: « Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe. » ( 1 ) Suka ce: « Dã mun san ( yadda ake ) yãƙi dã mun bĩ ku. » Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa.
168. Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: « Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba. » Ka ce: « To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya. »
169. Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. ( 2 ) Ana ciyar da su.
170. Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; « Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba. »
171. Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai.
172. Waɗanda suka karɓa ( 3 ) kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su.Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata ( 4 ) yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa.
173. Waɗanda mutãne ( 5 ) suka ce musu: « Lalle ne, mutãne sun tãra ( rundunõni ) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai ( wannan magana ) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: » Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ. « »
( 1 ) Ku tunkuɗe mana maƙiyã da duhunku, kõ dã ba ku yi yãƙi ba.
( 2 ) A cikin Hadisi an ruwaito cẽwa, Annabi yã ce Allah Yanã sanya rũhinsu a cikin cikkunantsuntsãye mãsu kõren launi, sunã tafiya da su a cikin Aljanna sunã ci daga 'ya'yan itãcenta da rãna, sa'an nan su kõma zuwa ga wasu fitillu waɗanda aka rãtaye a cikin inuwar Al'arshi.
( 3 ) Bayan kõmawar Musulmi daga Uhdu da miyãkun da suka sãme su, sai Annabi ya umurce su da fita a bãyan kãfirai, dõmin kada su yi tunãnin kõmãwa. Sai suka fita bãyansu, aka dãce kuwa Abu sufyãna ya umurci mutãnensa da kõmawa Madĩna dõmin su tumɓuke Musulmi. An yi Uhdu ta farko ran Asabat, sa'an nan suka fita a bãyansu a rãnar Lahadi, suka riskẽ su a Hamra'al Asad. Sai aka yi tawãfuƙi ( yarjẽjeniya ) tsakanin Annabi da Abu Sufyãna a kan a bar yãƙi a lõkacin, sai shekara mai zuwa, a haɗu a Badar. Allah Ya yabi Musulmi, da suka karɓa wannan kira, a cikin miyãkũ. Haka duka mai karɓawa irinsu, yã shiga a cikin irin wannan yabo har ya zuwa tãshin Ƙiyãma.
( 4 ) Kyautata yi shi ne tsarkake aiki dõmin Allah watau ihsani kõ ihlasi.
( 5 ) Yãƙin Badar na Uku, a cikinshẽkara ta huɗu yake, a watan Sha'aban. Badar kãsuwa ce babba ga ƙabĩlun Lãrabãwa a kõwace shekara. A bãyan Uhdu an yi alkawari da Abu Sufyãna, a kan a haɗu a Badr shẽkara mai zuwa.Sabõda haka sai Abu sufyãna ya fita daga Makka har ya sauka Marriz zahrãn, sai Allah Ya sanya masa tsõro a cikinzũciyarsa sai ya gamu da Nu'aima bn Mas'ũd el Ashja'iy, ya ce masa: « Ni nã yi alkawari da Muhammadu a kan muhaɗu a Kãsuwar Badar. Wannan kuwa shẽkar fari ce. Inã son sãɓãwar alkawarin ta zama daga gare shi, bã daga gare ni ba. Ka tafi Madĩna ka yi ƙõƙarin hana su fitõwa,zan bã ka rãƙuma gõma. » Sai Nu'aimu ya tafi Madĩna ya iske Annabi da Sahabbansa suna shirin fita. Sai ya ce musu: « Me kuke nufi? » Suka ce; « Alkawarin Abu sufyãna. » Sai ya ce: « Bã zã ku iya ba, dõmin kuwa sun tãra rundunõni sabõda ku. » sai Annabi ya ce: « Zan fita kõ da nĩ kaɗai ne. » Sai Annabi ya fita da mutum dubu da ɗari biyar, suka tafi Badar bãbu Abu Sufyãna. Suka ci kãsuwa suka kõmo.