Surah Al-Imran | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 73
Suratul Al-Imran from 174 to 180
174. Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma.
175. Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni.
176. Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.
177. Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi.
178. Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa.
179. Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai ( 1 ) Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba. ( 2 ) Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa. ( 3 ) Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.
180. Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar Ƙiyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
( 1 ) Watau Allah bã zai bar mutãne su ce: 'Mun yi ĩmãni, dabãki kawai ba,' sai Yã jarraba su Ya fitar da mũminan ƙwarai daga munãfukai. Sabõda haka Ya sanya rãnaiku kamar rãnar Uhdu wadda Allah Ya jarrabi mũminai da ĩta har haƙurinsu da ɗã'arsu suka bayyana, kuma munãfukai suka bayyana.
( 2 ) Allah bai sanar da gaibi ga mutãne waɗanda ba Annabãwa ba, sabõda haka bã ku iya sanin ĩmãnin mutum ko rashin ĩmãninsa, sai da alãmata wani aikĩ ko magana wadda take da ita za a iya yin hukunci da kãfirci ko ĩmãnĩ gamutum.
( 3 ) Allah Yã zãɓi wanda Ya sodaga manzanninSa, watau Yã zaɓi Annabi Muhammadu da ƙãrin daraja a kan sauran Annabãwa da falalarsa. Wannan ne mafificin yabo a gare shi.