Hausa translation of the meaning Page No 74

Quran in Hausa Language - Page no 74 74

Suratul Al-Imran from 181 to 186


181. Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: « Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu. » za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: « Ku ɗanɗani azãbar gõbara! »
182. « Wannan ( azãbar ) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyinsa ba. »
183. Waɗanda suka ce: « Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci. » Ka ce: « Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya? »
184. To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske.
185. Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar Ƙiyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra.Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi.
186. Lalle ne zã a jarraba ( 1 ) ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra.
( 1 ) Duk wanda ya tsayu da gaskiya ko umurni da alhẽri, ko hani daga abin da ba a so, to lalle ne sai an eũtar dashi, kuma ba shi da mãgani sai haƙuri, dõmin Allah, da nẽman taimako daga Allah, da kõmãwa zuwa ga Allah.