Hausa translation of the meaning Page No 8

Quran in Hausa Language - Page no 8 8

Suratul Al-Baqarah from 49 to 57


49. Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.
50. Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.
51. Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci ( da bauta masa ) .
52. Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa.
53. Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa.
54. Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: « Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. »
55. Kuma a lõkacin da kuka ce: « Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane, » sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo.
56. Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa.
57. Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; « Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. » kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.