Hausa translation of the meaning Page No 7

Quran in Hausa Language - Page no 7 7

Suratul Al-Baqarah from 38 to 48


38. Muka ce: « Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki. »
39. « Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne. »
40. Yã Banĩ Isrã'Ĩla ( 1 ) ! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na. Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.
42. Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane.
43. Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i.
44. Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba?
45. Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah.
46. Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne.
47. Yã banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa, wadda Na ni'imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan tãlikai.
48. Kuma ku ji tsron wani yini, ( a cikinsa ) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba.
( 1 ) Bãyan kiran mutãne gabã ɗaya zuwa ga addinin musulunci, sai kuma ya kẽɓance Yahũdu da kira zuwa ga addinin, dõmun sun banbanta da sauran kãfirai, sabõda ilminsu ga gaskiyar Musulunci. Yã gabata cẽwa jama'ar, kashi huɗu ce; mũminai, da kãfiran Lãrabãwan da bã zã su musulunta ba, da munãfukai da Yahũdu. Ya kira Yahũdu da Bani Isrã'ĩla, dõmin Ya tunãtar da su, cẽwa anã kiransu ne zuwa ga addini irin na ubansu kiransu Ya'aƙũbu bawan Allah.
41.