Hausa translation of the meaning Page No 80

Quran in Hausa Language - Page no 80 80

Suratul Al-Nisa from 15 to 19


15. Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su. ( 1 )
16. Kuma waɗanda ( mazã biyu ) suka je mata ( 2 ) daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai
17. Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa ( 3 ) to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
18. Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: « Lalle ne ni, na tũba yanzu, » kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi
19. Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha ( 4 ) bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa.
( 1 ) Ãyõyi na 15 da l6 an shãfe hukuncinsu wajen haddi da ãyar sũratun Nũr ta biya da Hadisin Rajami ga zawari da zawara waɗanda suka yi zina, kuma da bũlãla ɗari dakõrar babane namiji, da kuma bũlãla ɗari ga budurwa. Kuma ana jẽfe mai liwãɗi da wanda ake yi a kansa idan sun balaga, ko dã su banãwa ne. Ana ladabi ga mailiwãɗi da matãrsa, amma ba a kashe shi. Liwãɗi da wata mace kamar zina yake ga namijin.
( 2 ) Maza biyu mãsu je wa alfasha su ne mãsu yin liwãɗi da jũnansu.
( 3 ) Nan kusa, watau a gabãnin mutuwa.
( 4 ) Mugun halin da sharĩ'a ba ta yarda da shi ba kamar ƙiyokõ yãwon banza, a nan bãbu laifi ku hana su aure sai sun yi muku hul'i, kuma Allah Yã hana gãdon mãta kamar dũkiya. Sun kasance sunã yin haka, ba da sãke bayar da sadaki ba, domin dogara da wanda ubansa ya bãyar, sai su aurar da ita a kan haka ga wani ɗan'uwan mamacin, kõ kuma wanda suke so ya aure ta.