Hausa translation of the meaning Page No 81

Quran in Hausa Language - Page no 2 2

Suratul Al-Nisa from 20 to 23


20. Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari ( 1 ) to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bãyyananne?
21. Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenkuyã sãdu zuwa ga sãshe, kuma sun riƙi alkawari ( 2 ) mai kauri daga gare ku?
22. Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya.
23. An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi ( 3 ) a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
( 1 ) Ƙinɗãri, shi ne dũkiya mai yawa; ũƙiyya dubu gõma sha biyu, na azurfa.
( 2 ) Alkawarin riƙonsu da alhẽri ko kuma sallamarsu da kyautatãwa. Baƙara Ãya ta 231.
( 3 ) Ɗaurin aure a kan ɗiyayana haramta uwarta, amma ɗaurin aure a kan uwa,bã ya haramta ɗiyar sai in an yi duhũli da ita, kõ kuma an yi tamattu'i da ita.