Hausa translation of the meaning Page No 82

Quran in Hausa Language - Page no 82 82

Suratul Al-Nisa from 24 to 26


24. Da tsararrun auren ( 1 ) wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. ( Ku tsare ) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya ( 2 ) da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima.
25. Kuma wanda ( 3 ) bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, ( ya aura ) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga ( 4 ) sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan ( auren kuyanga ) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai.
26. Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a gabãninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima.
( 1 ) An haramta muku matan auren wasu maza, matuƙar mazansu ba su sake su ba, Musulmi ne kõ kuwa Kitãbãwa, sai fa idan kun kãmo su ne dagaƙasar da take ta abõkan gaba, a nan kunã iya tãkinsu haka, dõmin kãmu yã warware aurensu. Idan kun yi tamattu'ida wasu mãtã a kan kuskure, ba da aure ba, sai ku biya su sadãki a kan haka. An hana auren tamattu'i, watau yin aure zuwa ga ajali. Abdullahi bn Abbas ya ce yin sa yã fi zina.
( 2 ) Bãyan sadãkin da aka yankabãbu laifi ĩdan kun yi yardatayya da ƙãra wani abu a kan farilla, kuma bãbu laifi idan ita matar tã yarda da kãyar da ƙarin kõ kuwa shĩ mijin ya yarda da biyan ƙãrin.
( 3 ) Hukunce- hukuncen auren kuyanga ga wanda bai sãmi ĩkon auren'ya ba. Aibin auren kuyangi shi ne bautar da zuriya, domin bauta daga uwa take. Saboda haka bã ya halatta ga Musulmi ya auri baiwar kafiri, kome larurar da take ciki,sai dai ya saye ta daga gare shi.
( 4 ) Ku duka daidai kukewajen ĩmãni da Musulunci. Dubi kuma Ãli'Imrãna 195.