Hausa translation of the meaning Page No 83

Quran in Hausa Language - Page no 83 83

Suratul Al-Nisa from 27 to 33


27. Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma.
28. Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni.
29. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara, ( 1 ) fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne.
30. Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma wannan yã kasance ga Allah ( abu ne ) mai sauƙi.
31. Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci.
32. Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga dukkan kõme, Masani.
33. Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla ( 2 ) ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.
( 1 ) Hukuncin cin dukiyar mutane da ƙarya ko yaudara, haramun ne, domin yana kai ga mutane su kashe kansu.
( 2 ) A zãmanin Jahiliyya ana ƙullin amana a tsakanin ƙabilu ko a tsakanin mutum da wanimutum. Wannan ƙullin amãnar yakan haɗa har da sudusin dukiyar wanda ya mutu daga cikinsu. Wasu Musulmi sun shiga Musulunci a bãyan sun ƙulla irin wannan amãnar sabõda haka Allah Ya yi umurni da cika wannan alkawarin, kuma Ya kashe al'adar Ya musanya ta da hukunce- hukuncen Musulunci. Kuma ana fassara masu ƙullin rantsuwa da masu gudãnar da aikin rabon dũkiyar gãdo. Ana biyan su ijãrar wahalarsu daga kãwunan magãda kamar yadda ya kamata.