Hausa translation of the meaning Page No 86

Quran in Hausa Language - Page no 86 86

Suratul Al-Nisa from 45 to 51


45. Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma Yã isa Ya zama Mataimaki.
46. Daga waɗanda suka tũba ( Yahũdu ) , akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: « Munjiya ( 1 ) kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina ( da ma'anar 'ruɓaɓɓe' ) , ka tsare mu, » dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: « Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana, » haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan.
47. Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa.
48. Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma.
49. Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba.
50. Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne.
51. Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da gunki da Shaiɗan ( 2 ) kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: « Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya » ?
( 1 ) Yahũdu, ana kiran su da maganar Mũsã da ya ce wa Ubangiji, Mun tũba zuwa gare Ka, yã Allah, ( A'arãf, ãyã ta 155 ) ,dõmin izgili da suke yi na ƙin bin haddõdin Allah sunã karkatar da magana da asalin ma'anarta zuwa ga wata ma'ana ta izgili sunã cẽwa 'Mun ji' amma aikinsu yanã nũna cẽwa, 'sun ƙi' suke nufi. Kuma 'Ka jiya a wani wurin jiyãwa,' addu'a ce mai ɗaukar ma'anar alhẽri da ma'anar sharri, su kuwa sunã nufin ta sharrin. Haka kalmar 'rã'ina,' tanã da ma'anar 'tsãre mu,' ko 'saurãra mana', kuma tanã da ma'anar 'Yã ruɓaɓɓe.' Sunã nufin ma'anar ƙarshen.
wannan bayãni shi ma taimakõ ne ga Musulmi mãsu raunin hankali dõmin a tsare musu addininsu kamar yadda ake tsaron dũkiyarsu. An cũsa irin wannan mãkirci a wata addu'a da suke cewa 'Jauharatul Kamãli' inda suka siffanta wanda suke yi wa salãti da « asƙam » mafi cũta. Wannan tã yi daidai da kalmar rã'ina, ko ma ta fi mũni, dõmin rã'ina tanã da wata ma'ana ta yabo, ammaasƙam bã ta da wata, ma'ana sai ta zãgi kawai. Allah Ya tsare mu daga sharrin maƙiyan addini.
( 2 ) Jibti sunan kowane gunki ne.Ɗãgũtu sunan Shaiɗan ne mai ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, sheɗãnin da yake zama tare da gumãka ko waninsu, mutum ne ko aljani, dõmin ya ɓatar da mãsu raunin hankali, a cikin Yahũdu ko a cikin Musulmi.