Hausa translation of the meaning Page No 87

Quran in Hausa Language - Page no 87 87

Suratul Al-Nisa from 52 to 59


52. Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba.
53. Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba.
54. Ko suna hãsadar mutãne ( 1 ) ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.
55. To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.
56. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
57. Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, ( waɗanda ) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.
58. Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. ( 2 ) Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.
59. Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. ( 3 ) Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
( 1 ) Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah sun tabbata agare shi. An ce masa ɗan gidan Ibrahim domin Yahũdu su san shi ba kasasshe ba ne ga dangantaka, daga gare su. Kum bai fita ba daga tsãrin cẽwa Annabãwa mãsu Littãfi a bãyan Ibrãhĩm, daga zuriyarsa za su fito. Kuma sun san wannan a cikin littãfinsu, watau Attaura.
( 2 ) Talakãwa mutãne ne mãsu rauni a cikin hannuwan shugabanninsu. Su da dukiyarsu amãnõni ne na Allah a cikin hannuwan shugabanni, saboda haka tsaronsu da dukiyarsu, gwargwadon shari'a, da yin hukunci a tsakaninsu da ãdalci, bãyar da amãna ne ga mãsu ita.Wanda ya bi son zuciyarsa duka ga ɗayan waɗannan abũbuwa, to, yã yi yaudara ga Allah ke nan. Allah kuma zai kama shi da hukuncinmayaudari.
( 3 ) Haka su kuma mutãne talakãwa, amãna ce a kansu su yarda da hukuncin Allah da Manzonsa, a kome na al'amurransu da mu'ãmalõlinsu. Kumawãjibi ne a kansu su yarda da abin da aka hukunta a kansu daidai da sharĩ'ar Allah. Sai kuma idan sun sãɓa, to, sun yaudari amãnar Allah ke nan.