Hausa translation of the meaning Page No 88

Quran in Hausa Language - Page no 88 88

Suratul Al-Nisa from 60 to 65


60. Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga Ɗãgũtu ( 1 ) alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.
61. Kuma idan aka ce musu: « Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo » zã ka ga munãfukai ( 2 ) sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa.
62. To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, « Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa. » ?
63. Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.
64. Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, ( 3 ) sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.
65. To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.
( 1 ) Ɗãgũtu shi ne dukan mai yin dõkõki waɗanda ba dõkõkin Allah ba. Dukan wanda ya bi dõka wadda ba ta Allahba a cikin ibãda, ko wadda ta saɓa wa haddin Allah a cikin mu'ãmalõli na haƙƙõƙi ko na laifuka, to, ya shiga cikinwannan tarkon.
( 2 ) Miyãgun shugabanni mãsu karkatar da mũminai daga hukuncin Allah da hujjar wai suna nufin su daidaita domin a haɗa Musulmi da kãfirai ga hukunci; ta haka har kãfiri ya kasance mai yin hukunci a kan Musulmi. Su waɗannan masu yin haka ba Musulmi ba ne, munãfukan Musulmi ne. Musuluncinsu na bãki ne kawai, dã yã kai ga zũciya dã ba su yi ko tunãnin yardada haka ba. Allah Ya tsare mu daga sharrin Shaiɗan,
( 3 ) Wanda ya ƙi hukuncin Allah,ya yi laifi biyu, domin sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wannan ya nũna rashin ĩmãninsa da Allah da ManzonSa. Saboda haka ne ãyã mai bin wannan ta ce Musulmi bã suda ĩmãni sai sun yarda da Hukuncin Allah ga kome daga al'amurransu, kuma su yardada hukuncinsa, bã da jin wani ƙunci a cikin zukatansu ba.