Hausa translation of the meaning Page No 89

Quran in Hausa Language - Page no 89 89

Suratul Al-Nisa from 66 to 74


66. Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, « Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidãjenku, » dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa.
67. Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gunMu.
68. Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya.
69. Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda ( 1 ) da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya.
70. Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani.
71. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku ( 2 ) sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya.
72. Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa ( 3 ) . To idan wata masĩfa ta sãme ku, sai ya ce: « Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre da su ba. »
73. Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa, kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: « Yã kaitona! Dã na zama tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma! »
74. Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma.
( 1 ) Darajar ɗaukaka ga addini shi ne zama Annabi sa'an nan siddĩƙ, watau manyan sahabban kowane Annabi. Waɗannan darajõji biyu yanzu an rufe su daga kõwa, dõmin bãbu sauran Annabci wanda yake tãre da siddĩƙanci. Ta uku ita ce shahãda watau a kashe mutum a wurin yãƙi dõmin ɗaukaka kalmar Allah da tsare haƙƙõƙin Musulmi. Wannan ita ce maƙasudin abin faɗa a nan, dõmin abin da sũrar ke karantarwa, kuma dõmin ya zama shimfiɗar magana a kan darajar jihãdi da amfanõninsa. Ta huɗu zama sãlihi mai son abin da Allah Yake so kuma mai ƙin abin da Allah Yake ƙi.
( 2 ) Bã ya halatta Musulmi su zauna bãbu tattalin yãƙi da fitar da yãki ko hari a kan maƙiyansu, saboda abin da ke cikin wannan ãyar ta 71.
( 3 ) Siffar munãfuki ita ce ya ƙi fita zuwa yãƙi, kuma ya fãsar da waninsa, ya yi murnar hasãrar Musulmi, kuma ya yi baƙin cikin nasararsu, ya so a raba ganĩma da shi.