Surah An-Nisa | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 93
Suratul Al-Nisa from 92 to 94
92. Kuma bã ya kasancẽwa ( 1 ) ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan ( wanda aka kashe ) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne ( waɗanda ) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi ( wuyan ba ) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
93. Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, ( 2 ) to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma.
94. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya ( a cikin ƙasa ) , dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani. ( 3 ) Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: « Bã Musulmi kake ba. » Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni.Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.
( 1 ) Kisan kuskure bãbu ƙisãsi a cikinsa, sai dai biyan diyya da kuma kaffãra. Amma biyan diyya yana kan dukkan dangin mai kisan, gwargwadon ƙarfin su, shi ɗaya ne daga cikin su. Idan danginsa ba su isa ba, ko kuwa bãbu su, to, sai baitulmãli na Musulmi yabiya. Ana biyan diyya a cikin shekaru huɗu. Ana bãyar da ita ga magãdan wanda aka kashe. Amma kaffãra ita kam a kan mai kisan kawai takea kan tartĩbinta. Wanda ya kashe bãwa bisa kuskure zai biya ƙĩmarsa ga mai shi, kuma ana son ya yi kaffãra.
( 2 ) Wanda ya kashe mũminai da ganganci, kuma yana ƙudurcin halaccin kashe shi ɗin, to, shi kãfiri ne. Amma idan yana ƙudurcin haramein kisa, amma duk da haka ya kashe shi domin wata fã'ida ta dũniya, ko domin adãwa, to yana nan mũmini, hukuncinsa ƙisãsi. Surar Baƙara, ãya ta179.
( 3 ) Bayãnin cewa ana ɗaukar wanda aka ji ya yi kalmar shahãda mumini, sai fa idan an ga ya yi wani aiki, ko aka ji ya yi wata magana wadda take warware ma'anar kalmar shahadar, bãbu kuma wani tãwĩli ko jãhilcin da yake iya zama uzuri ga mai shi.