Surah Al-Fatihah Makki | Surah No: 1 - Ayat No : 7 word No : 29 - litter No : 139 - name : The Opening

Surah Al-Fatihah | from the moshaf in arabic uthmani

Listen mp3 Tafsir Arabic tafsir mokhtasar
English Indonesian French
German Hausa Spanish

Surah Al-Fatihah

Hausa translation of the meaning Page No 1

Quran in Hausa Language - Page no 2 2

Suratul Al-Fatihah from 1 to 7


Sũratul Fãtiḥa
Ãyõyinta 7 ne. Anã kiranta Uwar Littafi dõmin tã tãra ilmin da yake a cikin Alƙu’ãni a dunkule. Bãsmala a cikinta take ga ƙirã’ar Ãsim, ruwãyar Hafs, ammã banda ga kirã’ar Warsh.
1. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
2. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
3. Mai rahama, Mai jin ƙai;
4. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
5. Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
6. Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
7. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. ( 1 )
( 1 ) Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilmin tauhidi na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar dũniya mai dõgẽwa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma Kai muke nẽman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce- hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi, yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu, yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata.