Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 4
Suratul Al-Baqarah from 17 to 24
17. Misãlinsu ( 1 ) shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa ( na abin tsõro ) , Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.
18. Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa.
19. Ko kuwa kamar girgije mai zuba ( 2 ) daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!
20. Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.
21. Yã ku mutãne! Ku bauta ( 3 ) wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku !
22. Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa,kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.
23. Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra guda daga misalinsa ( Alƙur'ãni ) . Kuma ku kirãwo shaidunku ( 4 ) baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.
24. To, idan ba ku aikata ( kãwo sura ) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai.
( 1 ) Allah Yã bayyana misãlin munãfuki da misãlai biyu, na farko, kamar mutum a cikin duhu yanã kẽwaye da abũbuwan ban tsõro bai sani ba, sai ya hũra wuta, ta yi haske ya ga abũbuwan na ban tsoron sa'an nan wutar ta mutu, ta bar shi a cikin duhu, sai tsõron yahauhawu a kansa. Haka munãfuki yake a bãyan yayi iƙrãrida Musulunci, a kullum yanã cikin tsõron abin da zã acea kansa. Ana sifanta hasken wuta da hasken ĩmãninsa. Bayan kasken ya tafi, sai ya zama kurma, makãho, sabõda haka bã ya mãgantuwa.
( 2 ) Misãli na biyu munãfukai sunã kamar matafiya a cikin jẽjida dare, ruwa kuma ya samesu a cikin duhu, basu iya mõtsãwa saida walƙiya, watau ãyar da suke so, kuma ga jin tsoron tsãwa; watau bayãnin halãyensu a cikin Alƙurãni, bã su son su ji, har sunã sanya kãnun yãtsunsu sunã tõshe kunnuwansu dõmin kada su ji. Ganin ido da basĩra da jin kunne da na hankali duk ɗaya suke, Allah Yana iya karɓe su ya bar su a cikin ɗimuwa.
( 3 ) Bãyan ya gama faɗin karkasuwar mutãne da sifõfinsu, sai kuma Ya kira su gabã ɗaya zuwa ga bauta Masa, Shi kaɗai. Ma'anar bauta Masa shi kaɗai, kõwa ya ajiye al'ãdarsa ya koma ga hukuncin Allah kawai; umurni kõ hani. Wanda ya bi wani hukunci na alãdarsa, ya bar abin da Allah Ya ce, to, shi ya sanya wa Allah kishiya ke nan.
( 4 ) Gumãkan ku su ƙẽra sura mai kama da Alƙur'ãni wajen fasãha da tsãri da kãwo asirai. An ce wa gumaka shaidu dõmin sunã cẽwa su ne za su yi musu shaida a Rãnar Ƙiyãma, kuma su cẽce su, kuma ko da yaushe su na tãre da su.