Hausa translation of the meaning Page No 3

Quran in Hausa Language - Page no 3 3

Suratul Al-Baqarah from 6 to 16


6. Lalle ne waɗanda suka kãfirta ( 1 ) daidai ne a kansu,shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba.
7. Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma.
8. Kuma akwai daga mutãne wanda ( 2 ) yake cewa: « Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira. » Alhãli kuwa su ba muminai ba ne.
9. Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni,alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa!
10. A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya.
11. Kuma idan aka ce musu: « Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa, » sukan ce: « Mũ mãsu kyautatawa kawai ne! »
12. To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa.
13. Kuma idan aka ce musu: « ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni, » sukan ce: « Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni? » To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani.
14. Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni,sukan ce: « Mun yi ĩmãni. » Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, ( 3 ) sukan ce: « Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne. »
15. Allah Yana yin izgili ( 4 ) gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.
16. Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba.
( 1 ) Kashi na biyu daga cikin jama'a sũ ne kãfiran da suka dõge akan kãfircin su, babu wani gisshi kuma Allah Yã san bã zã su musulunta ba.
( 2 ) Kashi na uku su ne munãfukai da suka bayyana Musulunci da bãki amma zuciyarsu tanã a kan kãfici.
( 3 ) Kashi na hudu su ne Yahudãwa waɗanda suke sun san gaskiyar Annabcin Muhammadu da Manzancinsa, amma hãsada ta hana su su bi shi, sunã ƙõƙãrin ɓãta abin da ya zo da shi ta hanyar jẽfa shibhõhi a ciki, dõmin su kange mutãne daga shigarsa. Sabõda haka aka ce musu shaiɗãnu. Duk wanda ya san gaskiya amma kuma ya yi girman kai daga binta, to, shi ne shaiɗan, daga aljannu kõ dagamutane.
( 4 ) Allah Yanã mayar masu da sakamakon izgilinsu.