Surah Al-Baqarah Madani | Surah No: 2 - Ayat No : 286 word No : 6,144 - name : The Cow

Surah Al-Baqarah | from the moshaf in arabic uthmani

Listen mp3 Tafsir Arabic tafsir mokhtasar
English Indonesian French
German Hausa Spanish

Surah Al-Baqarah

Hausa translation of the meaning Page No 2

Quran in Hausa Language - Page no 2 2

Suratul Al-Baqarah from 1 to 5


Sũratul Bakara
Tana karantar da kira zuwa ga addĩni da yadda ake ginin sãbuwar al’umma daga mutãne dabandaban, na Jãhiliyya.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. M̃.
2. Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa. ( 1 )
3. Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.
4. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.
5. Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.
( 1 ) Yã sifanta Littãfi; watau Alƙur'ãni da kamãla ya ce « Wancan » maimakon « Wannan » dõmin mãsu son su yi aiki da shi, su ne mãsu taƙawa. Taƙawa na da sharuɗɗa biyu, su ne ĩmãni da aiki da abin da manzancin Annabi Muhammadu ya ƙunsa. Sa'an nan mutãne a farkon Musulunci ko a inda Musulunci yake sãbo, sun kasu kashi huɗu. Kashi na farko sũ ne mãsu taƙawa waɗanda aka faɗi sifõfinsu a nan.