Surah Al-Maidah | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 122
Suratul Al-Ma'idah from 83 to 89
83. Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: « Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni,sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida. »
84. « Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai? »
85. Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna ( waɗanda ) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa.
86. Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗancan ne abõkan Wuta.
87. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi. ( 1 )
88. Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi.
89. Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa ( 2 ) a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi ( a kansa ) . To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.
( 1 ) Haramta abin da Allah Ya halatta kõ kuwa halatta abin da Allah Ya haramta kãfirci ne, dõmin wanda ya ƙetare haddi da kansa, yã yi da'awar Ilãhiyya kõ Annabci, haka wanda ya bi shi a kanwannan abin, ya yi shirki da Allah, dõmin yã sãmi wani mai waɗansu dõkõki wanda bã Allah ba, kuma ya bi shi a kansu, ko kuwa ya bi wanimai da'awar annabci, bãyan Alƙur'ãni yã ce an rufe annabci daga Annabi Muhammadu, tsĩra da amincĩ su tabbata a gare shi.
( 2 ) Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah daistigfãri, kuma tanã sanya tsiya.