Hausa translation of the meaning Page No 123

Quran in Hausa Language - Page no 123 123

Suratul Al-Ma'idah from 90 to 95


90. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ( 1 ) ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.
91. Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?
92. Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya.
93. Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni,sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. ( 2 ) Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
94. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi.
95. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. ( 3 ) Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.
( 1 ) Yin cãca da shan giya da refu da kiban ƙuri'a, aikatar da su warware alkawari ne na hana cin dukiyar mutãne da bãɗi1i ( ƙarya ) , da tsaron salla da Allah Ya yi umurni a tsare; watau rashin taƙawa ke nan.
( 2 ) Yã maimaita faɗin taƙawa sau uku ga wanda ya tuba da shan giya da cãca dõmin ya nuna nauyinsu. Wanda ya shã giyakõ ya yi cãca, yã keta haddin Allah da alfarmar mutãne da darajar kansa. sai yã yi taƙawa daga waɗannan zai iya rabuwa da su. Tsare su yanã cikin cika alkawari a tsakãnin mutum da Allah da kuma mutãne da ransa.
( 3 ) Barin farauta a cikin Haramiyanã a cikin cikãwa da alkawari. wanda ya sãɓa sai ya yi fansa da biyan misãlin abin da ya kashe daga dabbõbin gida na jin dãɗi; watau a biya barewada akuya kõ tunkiya. Amma kuma sai an sãmi mutum biyu ãdalai sunhukunta abin da mutum zai bayar ɗin. Idan bã Ya da dabbar, sai ya biya ƙĩmarta da abinci, ya bai wakõwane miskĩni ɗaya mudu guda. Idan bã ya iyãwa kuwa sai ya yi azumi, kõwane mudu guda kwãna ɗaya, guntun mudu a biya shi da cikakken kwãna.