Hausa translation of the meaning Page No 129

Quran in Hausa Language - Page no 129 129

Suratul Al-An'am from 9 to 18


9. Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa.
10. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu.
11. Ka ce: « Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance. »
12. Ka ce: « Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa? » Ka ce: « Na Allah ne. » Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar Ƙiyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba. « »
13. « Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani. »
14. Ka ce: « Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, ( alhãli Allah ne ) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi? » Ka ce: « Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki. »
15. Kace: « Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina. »
16. « Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, ( Allah ) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya. »
17. « Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi. »
18. « Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani. »