Hausa translation of the meaning Page No 130

Quran in Hausa Language - Page no 130 130

Suratul Al-An'am from 19 to 27


19. Ka ce: « Wane abu ne mafi girma ga shaida? » Ka ce: « Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa,kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa? » Ka ce: « Bã zan yi shaidar ( haka ) ba. » Ka ce: « Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki. »
20. Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa ( 1 ) kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.
21. Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba.
22. Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: « Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa? »
23. Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: « Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba. »
24. Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su.
25. Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu ( Mun sanya ) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: « Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko. »
26. Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nĩsanta daga gare shi, kuma bã su halakarwa, fãce kansu, kuma bã su sansancẽwa.
27. Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: « Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai. »
( 1 ) Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda sukasan ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗanSallãmi ya ce wa Umar: « Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna. »