Hausa translation of the meaning Page No 14

Quran in Hausa Language - Page no 14 14

Suratul Al-Baqarah from 89 to 93


89. Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako ( 1 ) da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.
90. Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci; ( 2 ) kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa.
91. Kuma idan aka ce musu: « Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar. » Sai su ce: « Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu, » kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar ( da suka sani ) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su ( na Attaura ) Ka ce: « To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya? » ( 3 )
92. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi ( 4 ) ( daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.
93. Kuma a lõkacin da Muka riƙi ( 5 ) alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, ( Muka ce: ) « Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji » Suka ce: « Mun ji kuma mun ƙi. » Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: « Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni! »
( 1 ) Sunã cẽwa idan Annabin ƙarshen zãmaninsa ya zo, zã su yãƙi kãfiran Lãrabãwa da shi. Sunã zaton a cikinsu zai ɓullo. Sai ya fito a cikin Lãrabãwan.
( 2 ) Bisa ga zãlunci, watau hãsada. Sun yi hãsadar Allah Ya saukar da abin da Yake so na falalarSa a kan wanda Yake so, shi ne Muhammadu, a cikin Lãrabãwa.
( 3 ) Waɗannan Annabãwan da kuka kashe ko kuka ƙaryata a cikinku suke kũ ne aka saukar wa da abin da aka bã su, sabõda haka da'awarku ta cẽwa kunã ĩmãni da abin da aka saukar muku ƙarya ce.
( 4 ) Riƙo A nan ma'anarsa bautawa; watau kõmãwa ga maraƙi da ibãda, ku bar Allah, bãyan Musa ya nuna muku ãyõyin Allah, yana ƙãra ƙaryata maganarku, ta cẽwa kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku kawai. Dã kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku, dã waɗannan abubuwa ba su auku ba daga gare ku.
( 5 ) A lõkacin da aka bã su Attaura sai suka ƙi aiki da ita sai da aka ɓamɓari dutse aka ɗaukaka shi sama a kansu, idan ba su yi aiki da ita ba ya fãɗa kansu. Sai suka karɓa, sa'an nan daga bãya kuma suka warware dõmin haka Ya ce: « Suka ce: Mun jiyakuma mun ƙiya. » Hãsali dai Yahũdu sun ƙi aiki da Littãfinsu, Attaura.