Hausa translation of the meaning Page No 140

Quran in Hausa Language - Page no 140 140

Suratul Al-An'am from 95 to 101


95. Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma ( Shi ) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, ( 1 ) wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?
96. Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. vwannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani.
97. Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki- daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
98. Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki- daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta.
99. Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi ( kõren ) , ( 2 ) kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje- dumbuje makusanta, kuma ( Muka fitar ) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.
100. Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa ( Shi ) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.
101. Mafarin ( 3 ) halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?
( 1 ) Mai ĩmãni daga kãfiri kõ kãfiri daga mai ĩmãni, da mai arziki daga matalauci da matalauci daga mawadãci, sarki daga talaka da talaka daga sarki,da mai sanyi daga mai zãfi ko mai zãfi daga mai sanyi, haka dai ga kõme Allah Yanã fitar da kĩshiyarsa.
( 2 ) Allah na halitta kõren ganyedaga hasken rãnã, sa'an nan Ya halitta gãrin ƙwãyã daga kõren.
( 3 ) Shi ne wanda Ya fãri halittasu bã da Yã kõya daga wani ba. Sautin jan wasalin fa zaiyi sama dõmi bambanci daga mafãri watau sababin abu, ana mĩƙe sautin maddi a gare shi.