Hausa translation of the meaning Page No 144

Quran in Hausa Language - Page no 144 144

Suratul Al-An'am from 125 to 131


125. Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa ( 1 ) ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.
126. Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki- daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa.
127. Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majiɓincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.
128. Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya ( Yanã cẽwa ) : « Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne. » Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: « Yã Ubangjinmu! Sãshenmu ( 2 ) ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana! » ( Allah ) Ya ce: « Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani. »
129. Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.
130. Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: « Mun yi shaida a kan kãwunanmu. » Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.
131. Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai. ( 3 )
( 1 ) Mai tãkãwa zuwa sama ƙirjinsa ƙunci yake yi, sabõda iskar numfashi tanã raguwa gare shi. Kuma shi yanã shasshekar gajiya da rashin iska. Wannan ilmi yanã a cikin mu'ujizar Alƙur'ani.
( 2 ) Haka daĩ mai laifi a bãyan azãbar laifinsa ta tabbata a kansa bã ya ɓõyẽwar abin da yariga ya bayyanã, sai ya faɗa da kansa dõmin ya bayyanar da nadãmarsa a lõkacin da nadãma bã ta da amfãni.
( 3 ) Allah bã Ya halaka mutãne sabõda wani laifi, sai bãyan Ya aiki mai gargaɗi ya tãfiya yi musu gargaɗi, sun san laifinsu, sun ƙi bari, sa'an nan azãba ta jẽ musu.