Hausa translation of the meaning Page No 153

Quran in Hausa Language - Page no 153 153

Suratul Al-A'raf from 23 to 30


23. Suka ce: « Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra. »
24. Ya ce: « Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi. »
25. Ya ce: « A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku. »
26. Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa ( 1 ) a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!
27. Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku,shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.
28. Kuma idan suka aikata alfãsha ( 2 ) su ce: « Mun sãmi ubanninmu akanta. » Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita. « Ka ce: » Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah? « »
29. Ka ce: « Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa. »
30. Wata ƙungiya ( Allah ) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne.
( 1 ) Tufar da aka saukar, ita ce addinin Allah. Wanda ya riƙã shi da taƙawa, to, ya kyauta ƙawarsa.
( 2 ) Alfãsha ita ce dukan mugun aiki, watau abin da sharĩ'a ba ta zõ da shi ba, kõ dã an jingina shi ga addini, kamar yinɗawãfi tsirãra da bauta wa malã'iku da sãlihai, da yin kõwace ibãda ba bisa ga yadda Annabi ya kõyar da ita ba.