Hausa translation of the meaning Page No 158

Quran in Hausa Language - Page no 158 158

Suratul Al-A'raf from 58 to 67


58. Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, ( tsirinsa ) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗanda suke gõdẽwa.
59. Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: « Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma. »
60. Mashawarta ( 1 ) daga mutãnensa suka ce: « Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya. »
61. Ya ce: « Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu ! »
62. « Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba. »
63. « Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku? »
64. Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu.
65. Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: « Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba? »
66. Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: « Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata. »
67. Ya ce: « Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu! »
( 1 ) Kissar Nũhu da mutãnensa tanã nũna yanda Annabawa mãsu kãwo gaskiya ke yin faɗa da miyãgun mutãne mãsu ƙin gaskiya, sunã ƙõƙarin rufe ta haka kuma ƙissõshin da ke tafe a bãyanta sunã nũna yadda ƙarya ke faɗa da gaskiya, ta hanyõyi dabam- dabam.