Hausa translation of the meaning Page No 157

Quran in Hausa Language - Page no 157 157

Suratul Al-A'raf from 52 to 57


52. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki- daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani.
53. Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: « Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa? » Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu.
54. Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana!
55. Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka.
56. Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa.
57. Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi, ( 1 ) sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni.
( 1 ) Ya kamanta hadari da ruwa da Alƙur'ãni da abin da ya ƙunsa, da sifanta ƙasa busasshiya da jahilci, da zuciyar ĩmãni da gari mai kyau, da zũciyar kãfirci da mugun gari, kuma rãyuwa da ĩmãni da mutuwa da tãshi. Annabi ya ce: « Misãlin abin da Allah Ya aiko ni da shi na ilmi da shiriya kamar ruwa ne mai yawa, ya sãmi wata ƙasa. To, ta zama daga cikinta akwai mai kyau, ta karɓi ruwa, sa'an nanta tsirar da ciyãwa da tsãtse mai yawa. Kuma ta zama daga gare ta akwai rãfuka, suka riƙe ruwa Allah Ya amfãni mutãne da shi, suka sha, suka shãyar kuma suka yi shũka. Kuma daga cikinta akwai nau'i, faƙanƙani bã ya riƙon ruwa, kuma bã ya tsirar da ciyawa,wannan shi ne misalin wanda ya fahimci addinin Allah, kuma abin da Allah Ya aiko ni da shi, ya amfãne shi, ya sani kuma ya sanar, da wanda bai ɗauka kai ba gare shi, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wadda aka aiko ni da ita. » Kuma anã fahimtar cẽwa kullum akwai faɗa mai dõgẽwa a tsakãninsu, dõmin sũ, kĩshiyõyin jũna ne.