Hausa translation of the meaning Page No 170

Quran in Hausa Language - Page no 170 170

Suratul Al-A'raf from 156 to 159


156. « Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ,mun tũba zuwa gare Ka. » Ya ce: « AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne. »
157. « Waɗanda suke sunã bin Manzo, ( 1 ) Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla. yanã umurnin su da alhẽri kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yanã halatta musu abũbuwa mãsu daɗi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, waɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka taimake shi, kuma suka bi haske wanda aka saukar tãre da shi, waɗannan ne mãsu cin nasara. »
158. Ka ce: « Yã kũ mutãne! ( 2 ) Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. ( Allah ) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa. »
159. Kuma daga mutãnen ( 3 ) Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.
( 1 ) Bayãnin bisharar Attaura da Linjĩla game da Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi. Kuma bishãrar da Allah ya gaya wa Annabi Mũsã wurin Miƙatinsa tãre da mutãne saba'in, dõmin maganar ɗinke take.
( 2 ) Mutãne a nan, anã nufin Yahũdu da wasunsu. Anã kiran su zuwa ga abin da Attaura ta yi musu bishãra da zuwansa,a cikin sifõfin da ta sifantã Shi da su.
( 3 ) Anã nũna cẽwa duka yadda mutãne suka ɓãci, bã zã a rasa na kirki a cikinsu ba.