Hausa translation of the meaning Page No 171

Quran in Hausa Language - Page no 171 171

Suratul Al-A'raf from 160 to 163


160. Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: « Ka dõki dũtsen ( 1 ) da sandarka. » Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu. « Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. » Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.
161. Kuma a lõkacin da aka ce masu: « Ku zauna ga wannan alƙarya, ( 2 ) kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa. »
162. Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana ( 3 ) watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.
163. Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar ( 4 ) ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.
( 1 ) Watau dũtsen da ya gudu da tufafinsa ne a lõkacin da yake yin wanka dõmin a nũna waBanĩ Isra'ila, waɗanda suka sõke shi da gwaiwa, cẽwa lãfiya lau yake Kuma aka umurce shi da ɗaukar dũtsen, kuma yanzu aka umurce shi da ya dõke shi dõmin ruwa ya fito sabõda shansu.
( 2 ) Alƙaryar ita ce Baitil Maƙdis, bisa shugabancin Yũsha'u. 'Saryarwa,' watau a saryar mana da zunubinmu, yã Allah!, 'Shiga ƙõfa da sujada,' watau da tawãli'u.
( 3 ) suka musanya hiɗɗa da hinɗa: watau alkama. ( Aya ta 161 ) Sai aka saukar da azãba a kansu, sabõda haka wannan yã nũna cẽwa Allah ba ya son a musanya addininSa da kõme, sai dai mutum ya yi shi kamar yadda ya zo masa. Musanyawar umarnin, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya. Ma'anar hiɗɗa ita ce kãyar da zunubi.
( 4 ) Wata alƙarya anã ce da ita Ailata a bãkin gãɓar Bahr Al Kulzum a zãmanin Dãwũda, Allah ya umurce su a kan harshen Dãwũda su riƙi Jumma'a rãnar ĩdi, su yanke aiki a ciki,dõmin ibãda, sai suka ƙi Jumma'a suka zãɓi Asabar, ma'anarsa yankẽwa. To, sai Allah ya tsananta musu, Ya hana su farautar kĩfi a rãnar Asabar, Ya halatta musu shi, a saurankwãnukan mãko. Sai a rãnar Asabar, su sãmi kĩfi wani kan wani, amma sauran kwanuka bã su sãmunsa haka. Sai Iblis ya sanar da su ga su aikata matarar ruwa a gefen tekun, a rãnar Asabar, su bũde kifi ya shiga su rufe, har rãnar Lahadi su kãma. Sai garin ya kasu uku: kashi ɗaya suka yi farauta, wasu suka hana, sũ kuma suka yi gãru a tsakãninsu da mãsu yi, na uku ba su yi farautar ba kuma ba su hana ba. A bãyan 'yan kwãnaki sai aka mayar da mãsu farautar birai, sa'an nan suka mutu.