Hausa translation of the meaning Page No 172

Quran in Hausa Language - Page no 172 172

Suratul Al-A'raf from 164 to 170


164. Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: « Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani? » Suka ce: « Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa. »
165. To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci.
166. Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: « Ku kasance birai ƙasƙantattu. »
167. Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu ( Yahũd ) , zuwa, RãnarƘiyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
168. Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa.
169. Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar ( 1 ) wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: « Zã a gãfarta mana. » Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?
170. Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa.
( 1 ) Sifar ƙasƙantacciya ita ce kãyan dũniya na haram, kamar rashawa. An kira ta sifa dõmin bã aba ce mai tsayuwa da kanta ba, kuma bã sifar abin kirki ba, sai dai abin da yake halaka ne nan da nan. Tãke gaskiya faɗa ne da addini, watau yaƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya.