Hausa translation of the meaning Page No 173

Quran in Hausa Language - Page no 173 173

Suratul Al-A'raf from 171 to 178


171. Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse ( 1 ) sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, ( aka ce ) : « Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa. »
172. Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi ( alkawari ) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, ( Ya ce ) : « Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba? » Suka ce: « Na'am! Mun yi shaida! » ( ya ce ) : « Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne. » ( 2 )
173. Kõ kuwa ku ce: « Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa,Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata? »
174. Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki- daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa.
175. Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa ( 3 ) ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.
176. Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni.
177. Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta.
178. Wanda ( 4 ) Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
( 1 ) A lõkacin da Mũsã ya karanta wa Banĩ Isra'ila Attaura da hukunce- hukuncen da suke a cikinta, mãsu wuya gare su, sai suka ƙi yarda da ita. Allah Ya yanka dũtse daidai da garinsu, Ya ɗaukaka shi a kansu, ko su yi aiki da ita kõ ya fãɗa a kansu. Daga nan idan suna salla, sai su yi sujada da rabin gõshi a kan tsãgin hagu, sunã kallon dũtsen. Kuma yin sujada a haka ya zama sunnarsu har yanzu. Watau bã a iya tsare gaskiya daga yãƙin ƙarya sai an yi amfãni da wani ƙarfi.
( 2 ) Watau kada ku ce ba ku sanwannan alkawari ba.
( 3 ) Asalin ƙissar anã cẽwa daga Bil'amu ɗan Bã'ura ne;Allah ya bã shi ilmi, sai ya bar ilmin. Yanã daga cikin mãlaman Banĩ Isrã' ĩla, yã kasance wanda ake karɓar addu'arsa, sunã gabatar da shi a cikin tsanance- tsanance, sai Mũsã ya aike shi zuwa ga sarkin Madyana ya kirãye shi zuwa gaAllah. Sai sarkin ya yanka masa ƙasa, ya bã shi, sai ya biaddinin sarkin, ya bar addinin Mũsã. Ya zama misãli ga duk mãlamin da bai yi aiki da ilminsa ba. Idan mãlami ya halaka, to, yã fi Shaiɗan sharri dõmin haka shaiɗan yake binsa wajen taimakonƙarya a kan gaskiya.
( 4 ) An sifanta Musulmi da abin da aka sifanta Yahũdu da shi cẽwa a cikinsu akwai na kirki, kuma akwai miyãgu, dõmin yãƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya ya dõge.