Hausa translation of the meaning Page No 174

Quran in Hausa Language - Page no 174 174

Suratul Al-A'raf from 179 to 187


179. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.
180. Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. ( 1 ) Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa:zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.
181. Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma,da ita suke yin ãdalci.
182. Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
183. Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.
184. Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu? ( 2 ) shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.
185. Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To,da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?
186. Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa.
187. Sunã tambayar ka ( 3 ) daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: « Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam. » sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: « Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani. »
( 1 ) Waɗanda suke rõƙon Allah bã da sũnãyenSa mãsu kyau ba, sũ ne aka sifanta da dabbõbi, har dabbõbi sun fi su, dõmin dabba tanã gudun abinda yake cũtar ta, amma sũ ba su san abin da yake cũtar su ba, balle su guje shi. Kuma anã fahimtar cẽwa bã a rõƙon Allah da wani sũna Nãsa, idan bai kasance acikin sanayenSa mãsu kyau ba, sai fa idan ya zama a duaƙule ne, kamar a ce, « Ya Allah inã rõƙonKa da sũnayenKa waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba, » dõmin Hadĩsi ya nũna a yi haka. kiran Allah bã da sunãyenSa mãsu kyauba yana cikin yãƙi a tsakãnin ƙarya da gaskiya.
( 2 ) Watau, Annabi Muhammadu,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bã ya da hauka sai hankali, sabõda haka mãsu yin addini da hauka, kamar mãsu da'awar tasawwufi, ƙarya suke yi, sunã faɗa ne da gaskiya. Kuma sũkar mai wa'azi da sũnãye faɗada gaskiya ne.
( 3 ) Tambayar abin da Allah bai bayyana shi ba, kamar Rãnar Tãshin Kiyãma, yãƙi ne a tsakanin ƙarya da gaskiya. cẽwawani mutum yã san gaibi ko yanã iya kãwo alhẽri kõ ya tunkuɗe wani sharri, ƙarya ne, kuma faɗã da gaskiya ne.