Hausa translation of the meaning Page No 175

Quran in Hausa Language - Page no 175 175

Suratul Al-A'raf from 188 to 195


188. Ka ce: « Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. »
189. Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ( 1 ) ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: « Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya. »
190. To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki.
191. Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa?
192. Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka!
193. Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne!
194. Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!
195. Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: « Ku kirãwo abũbuwan ( 2 ) shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini. »
( 1 ) Asalin halitta, rai guda ce, watau Ãdam, Allah ya fitar da Hauwã'u daga Ãdamu, ya mayar da ita mãtarsa, daga gare su zũriya ta yaɗu, kuma ya zama sunnar rai, namijin ya natsu zuwa ga macen. Kuma daga nan zama ya ci gabahar idan mace ta yi ciki, bã ta damuwa da shi sai yã yi nauyi, ita da miji su dinga addu'a, sunã rõƙon Allah. Abãyan bukãtarsu tã biya sai su manta da Allah, su ɗõra jingina abũbuwa zuwa ga sabubbansu, su bar tunãnin Mai sabbabawa. Daga nan abu ya yi zurfi har ya kasance shirki; bauta wa wani tãre da Allah,yãƙi ne a tsakãnin da gaskiya da ƙarya.
( 2 ) Bãyar da tsoro da wani abinbautãwa ko jingina wata bukãta a gare shi, daika yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya.