Hausa translation of the meaning Page No 182

Quran in Hausa Language - Page no 182 182

Suratul Al-Anfal from 41 to 45


41. Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ( 1 ) ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi.
42. A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani.
43. A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza.
44. Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra.
45. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci ( 2 ) Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara.
( 1 ) Daga farkon sũrar har zuwa a nan, anã bayãnin cẽwa ganĩmar Badar bã ta kõwa ba ce fãce Allah da ManzonSa; to, a nan Yanã bayãyin yadda zã a raba dũkiyar, kuma wannan rabon, ya zama sunna ga dukkan dũkiyar ganĩma da Musulmi suka sãmu da yãƙi kõ hari.
( 2 ) Ambaton Allah bayyane yã fikyau a wurin yãƙi da wurin harama da hajji kõ umra, kuma da lõkacin da ake fitã zuwa ga masallacin ĩdi. Wurin da bã waɗannan wurãre uku ba, ambaton Allah, ya zama asirce yã fi kyau.