Hausa translation of the meaning Page No 195

Quran in Hausa Language - Page no 195 195

Suratul Al-Taubah from 48 to 54


48. Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo, ( 1 ) kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,
49. Kuma daga cikinsu ( 2 ) akwai mai cẽwa, « Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni. » To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.
50. Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce: « Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni. » Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki.
51. Ka ce: « Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara. »
52. Ka ce: « Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu ( 3 ) mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne. »
53. Ka ce: « Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai. »
54. Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.
( 1 ) Tun farkon zuwan Annabi aMadĩna mũnafukai sun yi ta yin kaidi dõmin su ɓãta al'amarin Annabi da Musulunci, suka kãsa, har gaskiya ta bayyana, suka kãma bakinsu dõmin rashin abin da zã su iya faɗã a yarda da shi.
( 2 ) Kuma a yanzu ga yãƙin Tabũka ( munafukai ) sun bayyana da irin uzurran da suke kãwowa dõmin kada su fita kamar mai cẽwa « To, Allah Ya hana zina, idan na fita nã gã mãtan Rũmãwa, bã zan iya yin haƙuri daga barinsu ba' sabõdahaka inã son a karbi uzurina kada a jẽfa ni a cikin fitina. » Bai sani ba. da wannan rashin fitar ya jẽfa kansa a cikin fitinar. Dõmin zã a bar shi tãre da mãtã, sũ da shi kawai.
( 3 ) Ɗayan abũbuwa biyu mãsu kyau, sũ ne mutuwa a kan shahãda kõ rinjaya da sãmun ganĩma da izza.