Hausa translation of the meaning Page No 196

Quran in Hausa Language - Page no 196 196

Suratul Al-Taubah from 55 to 61


55. Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.
56. Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.
57. Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga.
58. Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi.
59. Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce: « Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa ( zai bã mu ) . Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne. »
60. Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya ( matafiyi ) . Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
61. Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa « Shi kunne ( 1 ) ne. » Ka ce: « Kunnen alhẽri gare ku,Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku. » Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi.
( 1 ) Shi kunne ne, ma'anarsa, kome ka gaya masa Yanã gaskatawa, watau wai ba shi da wãyon gãne gaskiyã da ƙaryã. Sabõda haka Allah Ya ce: Kunnen alhẽri, watau ya san gaskiya kuma yana gaskata ta, kuma ya san ƙarya, ba ya aiki da ita.