Hausa translation of the meaning Page No 205

Quran in Hausa Language - Page no 205 205

Suratul Al-Taubah from 112 to 117


112. Mãsu ( 1 ) tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.
113. Bã ya kasancẽwa ( 2 ) ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.
114. Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi ( Ibrãhĩm ) cẽwa lalle ne shĩ ( ubansa ) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri.
115. Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne.
116. Lalle ne Allah Yanã ( 3 ) da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.
117. Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da ( 4 ) Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan ( Allah ) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su. aka bari a cikin duhu.
( 1 ) Sa'an nan kuma ya bayyanã a cikin wannan ãyã ta 112 siffõfin muminai waɗanda aka fuskantar da kiran nẽman ciniki da su.
( 2 ) Bayãnin umurni da yanke wa kãfirai, kõ da sun mutu, da barin yi musu addu'ar alhẽri.
( 3 ) Wannan ãyã tanã nũna cẽwa taklĩfin da Allah Yake azã wa bãyinSa na yãƙi da waninSa, bã dõmin ya wahalar da su ba ne. Yanã yi ne dõmin alhẽri a gare su, Shĩ Allah Mawãdaci ne, Yanã da ƙasa da sammai, kuma shĩ ne Mai yin halittar kõme.
( 4 ) Yã fãra gabãtar da cẽwa, « Allah Yã karɓi tũbar Annabi da waɗanda Ya ambata tãreda shi, » dõmin ya biyar ãyar da ke zuwa ta tũbar waɗanda suka yi zamansu, bã da wani uzuri ba, kuma sũ bã munãfuƙai ba, aka jinkirtar da maganar tũbarsu har a bãyan hõron kwãna hamsin bãbu mai yimusu magana, bisa hanin Allah. Kuma dã an ambaci karɓar tũbarsu kawai bã da an gabãtar da tũbar waɗanda suka fita ba, dã sai a ce sun fi waɗanda saka fita, dõmin an yi nassi a kan tũbarsu. Wanda aka yi nassi akan tũbarsa, yã fi wanda