Hausa translation of the meaning Page No 204

Quran in Hausa Language - Page no 204 204

Suratul Al-Taubah from 107 to 111


107. Kuma waɗanda ( 1 ) suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, « Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri » , alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa,su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
108. Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka. ( 2 ) Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa.
109. Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
110. Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima.
111. Lalle ne, Allah Ya saya ( 3 ) daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. ( Allah Yã yi ) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma.
( 1 ) Wata ƙungiyã ta munãfukai mãsu aiki dõmin tumɓuke ƙarfin Musulmi ta hanyar da bã a iya gãnẽwa da sauri. Kamarsu gina masallaci kusa da wani tsõhon masallãci da sũnan taimakon addĩni amma da nufin su raba jama'ar Musulmi,kuma sun sãmi wurin da zã su riƙa tãro da ɓõye kãyan yãƙi da shirin sharri ga Musulmi. Kamar ma'abũta Masjidil Darãr, wanda aka yi kusa damasallacin Kuba a Madĩna. Aikinsu bai tsaya ga lõkacin yãƙin Tabũka ba, sabõda haka aka ce: da bagẽwa ga wanda ya yãƙi Allah a gabãni, watau a gabãnin bayyanar fallasar munãfukai da yãƙin Tabũka.
( 2 ) Sunã son tsarkaka ta ɓõye da ta bayyane. Ta ɓõye sananniya ce: ita ce rashin munãfunci, kuma ta bayyane ita ce sunã kãma rũwa a bãyan sun karce kãshinsu da dũtse, kamar yadda ya zo a cikin Hadĩsi. Allah ne Mafi sani.
( 3 ) Bãyan bayãnin nau'ukan kãfirai da alãmõminsu da yadda zã a bi wajen yankẽwa da su, da barin fage ga muminai na ƙwarai, sai kuma Yã kirãyi muminai zuwa ga mubãya'a ga Allah, watau ciniki, sa'an nan Ya bayyana musu kuɗin saye da abin sayarwa, ya ce: « Allah Yã saya daga muminai. »