Hausa translation of the meaning Page No 206

Quran in Hausa Language - Page no 206 206

Suratul Al-Taubah from 118 to 122


118. Kuma ( Allah ) Yã karɓi tũba a kan ukun ( 1 ) nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce ( kõmãwa ) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
119. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya.
120. Bã ya kasancẽwa ( 2 ) ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.
121. Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa.
122. Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya. ( 3 ) Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita ( zuwa nẽman ilimi ba ) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna?
( 1 ) Sũ mutãne uku waɗanda aka jinkintar da al'amarinsu, a ãyã ta l06, sũ ne Ka'abu bn Mãliki da Marãratu bn Rabĩ'a el Umary, da Halãlu bn Umaiya el wãƙify. Sun ƙi fita, bã da wani uzuri ba, kuma a lõkacin da Annabi ya kõmo daga Tabũka, waɗandaba su fita ba suka tafi suka faɗi uzurõrinsu na rashinfitã. Annabi ya karɓa musu Kuma ya nẽma musu gãfara. Amma su ukun, suka faɗi gaskiya cẽwa sun zauna ne bã dõmin munãfunci ba, sai dai abin yã kasance haka kawai bã da wani uzuri ba. To, Annabi ya ce su dãkata, saiabin da Allah Ya ce a kansu. Aka hana kõwa ya yi musumagana a cikin Madĩna, harmãtansu na aure. Suka yi kwãna hamsin a cikin matsuwa,sa'an nan Allah Ya sauko da tũbarsu.
( 2 ) Bayãnin falalar mutãne da ke zaune a Madĩna tãre da Annabi, a lokacinsa kõ bãyansa.
( 3 ) Bãyan yã ƙãre bayãni a kan falalar da Allah Ya fĩfĩta mazauna Madĩna da ita, sabõda haka bã ya halatta a gare su susãɓa wa Annabi da zama a bãyan yã fita zuwa yãƙi. Sa'annan kuma ya yi idiraki da ishãrar cẽwa fitã zuwa yãƙi farillar kifãya ce; wasu sunã ɗaukẽ wa wasu. Kuma bã ya kyautuwã a ce kõwa ya zama sojan yãƙi, a bar sauran ayyuka na lalũrar rãyuwa kamar fita nẽman ilmi, shi ma farillar kifãya ne tĩlas wasu su fita zuwa nẽmansa dõmin idan sun kõma ga mutãnensu sai su karantar da su. Hikimar ãyar tã fãra da maganar fita zuwa yãƙi kuma ta ƙãre da sakamakon kõmõwa daga makaranta dõmin nunawar fita zuwa gare su duka wajibi ne: Wanda wani ke iya ɗauke wa wani. Allah ne Mafi sani.