Hausa translation of the meaning Page No 207

Quran in Hausa Language - Page no 207 207

Suratul Al-Taubah from 123 to 129


123. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar ( 1 ) ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.
124. Kuma idan aka saukar ( 2 ) da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: « Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni? » To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra ( da ita ) .
125. Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai.
126. Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba?
127. « Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, ( su ce ) : » Shin, wani mutum yanã ganin ku? « Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtansu,dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta. »
128. Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo ( 3 ) daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
129. To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma.
( 1 ) Bayãnin yadda ake yin yãƙi ne; bã a fãɗa wa dukkan maƙiyã gabã ɗaya, na kusa da na nẽsa. Sai an farada na kusa tukuna sa' nan nan a dinga fãɗaɗãwa.
( 2 ) Taƙaitãwa da ƙãrin tanbĩhi ga abin da sũrar ta ƙunsa.
( 3 ) Bayãnin rahamar Allah gameda aiko Manzõ daga cikin mutãne, cẽwa wata falala ce a gare su. Kuma shi Manzon nan ɗan'uwansu ne wanda bã ya son su da wani abu sai alhẽri, idan sun gãne dã sun bĩ shi, kuma idan ba su gãne bã, to, Allah Yã tsare shi daga sharrinsu, kuma Yã isarmasa.