Surah Yunus | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 216
Suratul Yunus from 62 to 70
62. To, Lalle ne masõyan ( 1 ) Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba.
63. Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.
64. Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira.Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma,
65. Kada maganarsu ( 2 ) ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani.
66. To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa ( ga Allah a MulkinSa ) . Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai.
67. Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji.
68. Suka ce: « Allah Ya riƙi ɗa. » Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah?
69. Ka ce: « Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba. »
70. Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.
( 1 ) Waliyyin Allah, shi ne masõyin Allah da sharaɗin ya zama mumini mai taƙawa watau yanã aiki da abin da Allah Ya umurce shi, kuma yanãbarin abin da Allah Ya hana shi, bisa harshen Annabinsa wanda yake biya. Bãbu ƙarin kõme bãbu ragi. Bushãrarsu, ita ce yabon mutãne a gare su, kõ kuma a lõkacin mutuwarsu malã'iku su riƙa yi musu bushãra da gamuwa da Ubangijinsu, kõ kuma a cikin kabari wajen tambaya. Allah ne Mafi sani.
( 2 ) Maganarsu ta izgili a gare ka. Idan Allah Ya ɗaukakã ka, bãbu mai iya hanãwa dõmin Shi kaɗai ne Mai izza kuma sai inda Ya sanya ta ga wanda Ya so.