Hausa translation of the meaning Page No 233

Quran in Hausa Language - Page no 233 233

Suratul Hud from 98 to 108


98. Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu.
99. Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar ( 1 ) da ake yi musu.
100. Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe. ( 2 )
101. Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma ( gumãkan ) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra.
102. Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani.
103. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.
104. Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye.
105. Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki.
106. To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta.
107. Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi.
108. Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama ,a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa.
( 1 ) Kyautar la'ana ita ce wadda ake la'antar su da ita a dũniya da Lãhira.
( 2 ) Daga nan zuwa ƙarshen sũra ta'alĩƙi ne dõmin farkarwa. Mai tsayi, watau tana nan tsaye, alãmõminta ba su ɓãce ba, kuma akwai waɗanda suka halaka kamar karan da aka girbe.