Hausa translation of the meaning Page No 234

Quran in Hausa Language - Page no 234 234

Suratul Hud from 109 to 117


109. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba.
110. Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã ( 1 ) wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.
111. Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa ( sakamakon ) ayyukansa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa.
112. Sai ka daidaitu ( 2 ) kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
113. Kada ku karkata ( 3 ) zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.
114. Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ( 4 ) ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.
115. Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa. ( 5 )
116. To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su ( sun yi hanin ) . Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi.
117. Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa. ( 6 )
( 1 ) Yahũdãwa sun sãɓa wa jũna acikin littattafan da aka bai wa Mũsã. To, ku Musulmi kada ku bi hanyarsu, har ku sãɓawa Allah, har abin da ya sãme su ya sãme ku.
( 2 ) Wannan ãyã tanã hana dukan bidi'a a cikin addini. Tun da ba a yarda Annabi ya ƙara ra'ayinsa ba sai dai ya bi umurnin Allah kamar yadda Ya yi umurnin, kuma haka ne Ya umurci wanda ya bi Annabi. Sabõda haka mai sãɓa wa umurnin Allah da ƙãri ko ragi, bã ya cikin mabiyan Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
( 3 ) Ba ya halatta ga Musulmi yakarkata zuwa ga kãfirai kamar yaddabã ya halatta ya karkata a cikin addininsa. Wannan shĩ ne babban makãmi a kan mãƙĩya.
( 4 ) Tsayar da sallõli farillai tãre da Lĩman a cikin masallatai shĩ ne zikiri ga mai son zikiringaskiya. Ayyukan ƙwarai sunã shãfe miyãgu.
( 5 ) Haƙuri a kan ibãda wãjibi ne, haka kuma kyautatãwa, wãtau shĩ ne yin kõwãne aiki na ibãda tsantsa kamar salla kõ na ma' amala kamar ciniki da aure, dõmĩn Allah kawai. An yi wa wannan fanni na biyusũna da « Tasawwuf » , bidi'a ne dõmin bai taho daga sunna ba. Asalinsa « theosophy » daga lugar Ajam, ma'anarsa nẽman hikima ta Allah a hãlin kẽɓance kai a cikin kaɗaita da wasu aikace- aikace na ibada, kamar girka ga 'yanbõri.
( 6 ) Wannan ãyã da ta sama da ita sunã nũna muhimmancin wa'azi a cikin kõwane hãli na al'umma, dõmin tsarẽwar zamanta al'umma.